Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA: Daga titin Damavand zuwa dandalin Azadi, zuwa kowane titi da ƙaramin titi da ka duba, akwai kogin al'umma wanda ya haɗa soyayya kauna da fushi. Miliyoyin mutane masoya wanda idanunsu suka cika da nauyin baƙin ciki amma hannayensu sun cike da ƙarfen azama. Sun zo ne don raka gawar jagora shahidinsu mai tsarki, amma abin da ya ɗauki hankalin kowane mai kallo a cikin wannan babban taro kuma ya sa duniya ta girgiza, shi ne kogin tutoci jajaye marasa iyaka.
Tutoci jajaye waɗanda a yayin kaɗasu, ana jin karar takobi. Tutoci jajaye waɗanda kowane zare da zaren su ke shelanta: "An zubar da jini a nan. Ramuwa Fansa wajibi ne a nan." Waɗannan tutoci, suna da saƙo ɗaya, saƙo ɗaya kawai: Mu masu neman fansar jinin jagoranmu ne. Wannan jini ba zai ma na share shi ba. Wannan jini ba zai kasance ba tare da ramuwa ba. Wannan jini zai karbi fansa daga kan dukkan girman kai na duniya.
A al'adunmu, a addininmu, tuta ja tana nufin neman fansar jini. Tana nufin ramuwa. Tana nufin mun tashi don neman fansar jinin wanda ake zalunta. Wannan tuta, ita ce tutar da ta taɓa kaɗawa a saman yunkurin Mukhtar. Mukhtar Ath-Thaqafi, wannan zakin adalci, wanda bayan lamari mai ɗaci na Karbala, ya mayar da makoki da hawaye zuwa takobi, kuma ya ɗauki fansa daga kowane ɗayan masu kisan Imam Hussain (A.S). Ya nuna wa duniya cewa jinin wanda ake zalunta yana kawar da zaman lafiya na azzalumi. Ya koya wa tarihi cewa idan azzalumai sun sami ƙarfin hali na zubar da jini mai tsarki, to dole ne su sani cewa akwai masu neman fansa a kan hanya waɗanda za su hana su barci lafiya.
A yau Iran ma tana faɗin hakan. A yau wannan al'umma, ita ce magajiyar Mukhtar. A yau wannan al'umma, ta kalli sararin sama kuma tana jira. Tana jiran Mukhtar. Tana jiran yunkurin adalci. Tana jiran wanda zai tashi ya ɗauki fansar jinin jagora shahidinmu, daga Trump da Isra'ila masu laifi, daga shugabannin girman kai na duniya. A yau dukan Iran Mukhtar ce, dukan Iran tana shirye don ɗaukar fansa daga Yazid na zamani.
Mun ɗaga waɗannan jajayen tutoci kuma ba za mu sauke su ba, sai an ɗauki cikakkiyar fansa. Mun yi wannan shelar ta "Ya Latharatul Husain" kuma ba za mu yi shiru ba, sai mun samu ramuwar wannan jini daga kowane ɗayan azzalumai. Mun haɗiye hawayenmu don shelarmu ta fi ƙarfi. Mun mayar da makoki zuwa yunkuri don ƙarfinmu ya ƙaru.
Fiye da watanni huɗu kenan wannan al'umma, tana cikin baƙin ciki da ɓacin rai, tana zubar da hawaye a tituna. Amma a yau, waɗannan hawaye ba sa gudana a kan kunci; waɗannan hawaye sun zama wuta. Wutar da ke ci a ƙiraza kuma nan ba da jimawa ba za ta kama masu kisan. Zukatan da suka karye na wannan al'umma, ba za su sami kwanciyar hankali ba sai da ramuwa. Raunukan wannan al'umma, ba za su warke ba sai da halakar makiya.
Muna shelanta: Wannan jini ba zai kasance ba tare da martani ba. Mun tashi kuma za mu ci gaba da kasancewa. Muna jira. Muna jiran hannayen ƙarfi na mai ɗaukar fansar Allah. Muna jiran tashin Mukhtar. Kuma a ranar da Mukhtarinmu ya tashi, duniya za ta ga yadda ake yanke kan girman kai na duniya, da kuma yadda farin ciki zai dawo a zukatan wannan al'umma mai makoki.
Ya Mukhtar, ka tashi. Ya yunkuri, ka tashi. Waɗannan jajayen tutocin, waɗannan kururuwar neman fansar jini, waɗannan miliyoyin mutane masu jira, duk suna kiran ka. Ka zo ka ɗauki fansar jinin jagoranmu daga shugabannin kafirci da girman kai. Ka zo ka tsarkake duniya daga zalunci.
Mu masu neman fansar jini ne. Mu masu jira ne. Za mu tashi. Wannan ba alkawari ba ne; wannan kaddara ce.
Zahra Salehi Far, MSc a fannin Alƙur'ani da Hadisi, ɗalibar digiri na biyu a fannin Gudanar da Kafofin Yada Labarai a Jami'ar Baqiril-Ulum.
Fassara: Editan ABNA Hausa
Your Comment